A baya-bayan nan ne dai wannan mahardacin kur’ani dan kasar Libya ya halarci gasar haddar kur’ani ta kasa da kasa karo na 22 da aka gudanar a kasar Rasha, inda ya samu matsayi na daya a gasar.
Kashi na karatun tertyl na wannan hafiz na kasar Libya daga aya ta 67 da 68 a cikin suratul Ma'idah, wanda aka gudanar a gasar kur'ani ta kasar Rasha.